Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, manyan kwamandojin rundunonin sojojin Iran sun gana da Jagoran Ƙoli na Juyin Juya Halin Musulunci kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ƙasar, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i.
A yayin ganawar, Jagoran ya bayyana cewa kasancewa cikin shirin yaƙi cikin hikima domin fuskantar maƙiya da ƙarfi yana daga cikin muhimman abubuwan da ake buƙata wajen samar da cikakken ƙarfin hana maƙiya kai hari.
Ya kuma ba da umarnin cewa duk wani mataki ko nau'in barazana daga maƙiyi dole ne ya fuskanci martani cikin gaggawa, mai tasiri, kuma ba tare da takaita martanin ga wani yanki na ƙasa ko wuri ba.
Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i ya jaddada cewa, idan maƙiya suka sake fara kai hare-haren soji ko na ta'addanci, to rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da al'ummar Iran ne za su ƙayyade lokacin da kuma yanayin da za a kawo ƙarshen wannan yaƙi.
Babban Kwamandan Rundunar Sojin ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirrin soja, da zurfafa tsarin tsaron cikin gida a fannoni biyu na dabarun yaƙi da hanyoyin gudanar da ayyukan soja.
Haka kuma, ya bukaci a bunƙasa ƙarfin tsaro da kariya na zamani ta hanyar amfani da sabbin fasahohi, tare da ƙarfafa ƙarfin imani da ruhin gwagwarmaya a tsakanin dakarun soji.
Ya kuma jaddada cewa, wajibi ne a ci gaba da ƙoƙari ba dare ba rana wajen samar da buƙatun rayuwa da kuma tallafa wa rundunonin sojin ƙasar.
A wani ɓangare na umarnin da ya bayar, Jagoran ya buƙaci a sabunta jerin wuraren da ake ɗauka a matsayin manufofin soja, ta yadda za a haɗa da nau'o'in dukiyoyi da kadarorin maƙiyan Amurka da Isra'ila, na zahiri da waɗanda ba na zahiri ba, cikin wuraren da rundunar sojin za ta iya kai wa.
Jagoran ya bayyana cewa goyon bayan al'umma ga rundunar sojin ƙasa yana daga cikin manyan ginshiƙan hana baƙin ƙasashe masu adawa da Iran da kuma masu yi musu aiki a cikin ƙasar samun damar cimma manufofinsu.
Ya ƙara da cewa kasancewar al'ummar Iran a filayen fafatawa tsawon watanni takwas wani ci gaba ne na kariyar ƙasa da suka yi tsawon shekaru takwas a baya.
Ya bayyana cewa kamar yadda dakarun soji, 'yan sanda da rundunar Basij suka jajirce wajen kare ƙasar, al'umma ma ta taka muhimmiyar rawa wajen kare cikakken yankin ƙasar Iran da tsarin Jamhuriyar Musulunci, kuma za ta ci gaba da hakan.
Jagoran na Juyin Juya Halin Musulunci ya kuma yaba da jajircewa da kuma tsayuwar dakarun Gwagwarmaya (Muƙawama) a ƙasashe daban-daban.
Ya bayyana cewa haɗin kai tsakanin sassa daban-daban na wannan runduna ta gwagwarmaya yana daga cikin muhimman abubuwan da za su taka rawa wajen tsara sabon tsarin siyasa da tsaro a yankin Yammacin Asiya.
Ya kuma bayyana fatansa na cewa wannan sabon tsarin siyasa da tsaro zai zama wata dama ta ƙara ƙarfafa haɗin kan al'ummomi da gwamnatocin ƙasashen Musulunci, domin samar da sabuwar wayewar Musulunci.
A yayin ganawar, Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran, Laftanar Janar Abdullahi, Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ƙasa, Manjo Janar Hatami, da Babban Kwamandan Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Wahidi, sun gabatar da rahotanni ga Jagoran Ƙoli.
Rahotannin sun ƙunshi halin shirin ko-ta-kwana da kariyar da dakarun ƙasar suke yi a gabar tekun Fasha, wuraren ayyukan soja na mashigar Hormuz, Tekun Oman, da kuma iyakokin arewa maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar.
Sun kuma gabatar da rahoto kan yadda aka ƙara samar da makamai da alburusai iri-iri da dama fiye da yadda ake samarwa a baya, ciki har da makaman bincike, na tallafa wa ayyukan soja da kuma na yaƙi.
A ƙarshen ganawar, Jagoran Ƙoli na Rundunar Sojin ya bayyana farin cikinsa da ayyukan da aka gudanar. Ya kuma buƙaci manyan kwamandojin soji da su isar da saƙon godiyarsa da jin daɗinsa ga dukkan jami'an rundunonin soji, 'yan sanda, dakarun Basij, ma'aikatan waɗannan hukumomi, Ma'aikatar Tsaro da kuma iyalansu.
Ra'ayinka